Acts 9

Tuban Shawul

1Ana cikin haka, Shawul ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist 2ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa majamiʼun Damaskus, don in ya sami wani a wurin wanda yake bin wannan Hanya, ko maza ko mata, yǎ kama su a matsayin ʼyan kurkuku yǎ kai Urushalima. 3Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi. 4Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawul, Shawul, don me kake tsananta mini?”

5Shawul ya yi tambaya, ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?”

Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.”
6“Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”

7Mutanen da suke tafiya tare da Shawul suka rasa bakin magana; sun ji muryar amma ba su ga kowa ba. 8Shawul ya tashi daga ƙasa, amma saʼad da ya buɗe idanunsa bai iya ganin wani abu ba. Saboda haka aka kama hannunsa aka yi masa jagora zuwa cikin Damaskus. 9Kwana uku yana a makance, bai ci ba bai kuma sha kome ba.

10A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi, ya ce, “Ananiyas!”

Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”

11Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarsus mai suna Shawul, gama ga shi yana adduʼa. 12Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don ya sāke samun ganin gari.”

13Ananiyas ya amsa, ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima. 14Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don ya kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.”

15Amma Ubangiji ya ce wa Ananiyas, “Je ka! Wannan mutum zaɓaɓɓen kayan aikina ne don ya kai sunana a gaban Alʼummai da sarakunansu da kuma a gaban mutanen Israʼila. 16Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.”

17Saʼan nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawul, sai ya ce, “Ɗanʼuwana Shawul, Ubangiji-Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan-ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.” 18Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗo daga idanun Shawul, ya kuma sāke iya ganin gari. Sai ya tashi aka kuma yi masa baftisma, 19bayan ya ci abinci, sai sāke samun ƙarfi.

Shawul a Damaskus da Urushalima

Shawul ya yi kwanaki masu yawa tare da almajiran da suke a Damaskus.
20Nan take ya fara waʼazi cikin majamiʼu cewa Yesu Ɗan Allah ne. 21Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki suka ce, “Ba shi ne mutumin da ya ta da na zaune tsaye a kan masu kira bisa ga wannan sunan a Urushalima ba? Ba ya zo nan ne don ya kai su a matsayin ʼyan kurkuku ga manyan firistoci ba?” 22Duk da haka Shawul ya yi ta ƙara ƙarfi, ya kuma rikitar da Yahudawan da suke zaune a Damaskus, ta wurin tabbatar musu cewa, Yesu shi ne Kiristi.

23Bayan kwanaki masu yawa, sai Yahudawa suka haɗa baki su kashe shi, 24amma Shawul ya sami labarin shirinsu. Dare da rana suka yi fakonsa a ƙofofin birnin don su kashe shi. 25Amma almajiransa suka ɗauke shi da dare suka saukar da shi a cikin kwando ta taga a katanga.

26Da ya zo Urushalima, ya yi ƙoƙarin shiga cikin almajiran amma dukansu suka ji tsoronsa, ba su gaskata cewa tabbatacce shi almajiri ba ne. 27Amma Barnabas ya ɗauke shi ya kawo shi wurin manzanni. Ya gaya musu yadda Shawul a kan hanyarsa ya ga Ubangiji kuma cewa Ubangiji ya yi magana da shi, da yadda a Damaskus ya yi waʼazi ba tsoro a cikin sunan Yesu. 28Saboda haka Shawul ya zauna tare da su yana kai da kawowa a sake a cikin Urushalima, yana magana gabagaɗi a cikin sunan Ubangiji. 29Ya yi magana ya kuma yi muhawwara da Yahudawa masu jin Helenanci, amma suka yi ƙoƙarin kashe shi. 30Saʼad da ʼyanʼuwa suka sami labarin wannan, sai suka ɗauke shi zuwa Kaisariya suka aika da shi Tarsus.

31Saʼan nan ikkilisiya koʼina a Yahudiya, Galili da kuma Samariya ta sami salama. Ta yi ƙarfi; ta kuma ƙarfafa ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ta ƙaru sosai tana rayuwa cikin tsoron Ubangiji.

Eniyas da Dokas

32Da Bitrus yake zazzaga ƙasar, sai ya je ya ziyarci tsarkakan da suke a Lidda. 33A can ya tarar da wani mutum mai suna Eniyas, shanyayye wanda yake kwance kan gado shekara takwas. 34Sai Bitrus ya ce masa, “Eniyas, Yesu Kiristi ya warkar da kai. Tashi ka naɗe tabarmarka.” Nan da nan Eniyas ya tashi. 35Duk waɗanda suke zama a Lidda da Sharon suka gan shi suka kuma juyo ga Ubangiji.

36A Yoffa akwai wata almajira mai suna Tabita (wanda, in aka juya, shi ne Dokas
Da Tabita (Da Aramayik) da kuma Dokas (Da Helenanci) suna nufin barewa.
), ita mai aikin alheri ce kullum, tana kuma taimakon matalauta.
37A lokacin nan ta yi rashin lafiya ta mutu, aka kuma yi wa gawanta wanka aka ajiye a wani ɗaki a gidan sama. 38Lidda yana kusa da Yoffa; saboda haka saʼad da almajirai suka ji cewa Bitrus yana a Lidda, sai suka aiki mutum biyu wurinsa su roƙe shi cewa, “In ka yarda ka zo nan da nan!”

39Sai Bitrus ya tafi tare da su, saʼad da ya iso sai aka kai shi ɗakin saman. Duka gwauraye suka tsaya kewaye da shi, suna kuka suna nunnuna masa riguna da kuma waɗansu tufafin da Dokas ta yi yayinda take tare da su.

40Bitrus ya fitar da su duka daga ɗakin; saʼan nan ya durƙusa ya yi adduʼa. Da ya juya wajen matacciyar, sai ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe idanunta, ta ga Bitrus sai ta tashi zaune. 41Ya kama ta a hannu ya taimake ta ta tsaya a ƙafafunta. Saʼan nan ya kira masu bi da kuma gwaurayen ya miƙa musu ita da rai. 42Wannan ya zama sananne koʼina a Yoffa, mutane da yawa kuma suka gaskata da Ubangiji. 43Bitrus ya zauna a Yoffa na ɗan lokaci tare da wani mai aikin fatu mai suna Siman.

Copyright information for HauSRK